Categories
Sauran Labarai Tsaro

Hotuna: Dakarun sojin Najeriya sun kashe Boko Haram da dama

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa, dakarun sojin Najeriya sun ragargaji mayakan Boko Haram da suka ti yunkurin kaiwa Sojojin Harin ba zata.

Rundunar sojin Lafiya Dole dake yaki da Boko Haram a yankin na Maiduguri ta samu bayanan harin na Boko Haram tun kamin su kaishi dan haka ta shirya da Jiragen yaki da dakarunta na kasa, kamar yanda sanarwar da Hedikwatar tsaron ta fitar ta shafinta na Twitter ya bayyanar.

An sha gumurzune a Gajigana dake karamar hukumar Nganzai ta jihar Borno, An latata motar yaki 1 ta mayakan Boko Haram din inda suka gudu suka bar 2,an kuma kwato makamai da suka hada da bindigu da harsasai, da bamabamai da aka kera da hannu dadai sauransu.

Leave a comment