Categories
Siyasa

HON. NASIRU NUHU RIMI YAGANA DA DATTAWAN YANKIN TORO JAMA’AH

A yau  talata 8 ga watan feberu, Hon Nasiru Nuhu Rimi yagana da (Central working Committee) na Neman yakin cin zabensa a garin Nabardo dake Karamar Hukumar Toro JIhar Bauchi.

Shugaban Yakin neman Zabensa na (CWC), Hon. Bamboy Nabardo yayi jawabi dangane da Yadda wanna tafiya ke samun cigaba ta ko Ina a fadin Yakin toro Jama’ah.

Yakuma shaida wa Hon. Nasiru Nuhu Rimi dangane da wannan tafiya mai Albarka Babu gudu Babu ja da Baya sabida cancantansa dakuma Hidimtawa Al-ummah da Fadi tashin da yakeyi din ganin wannan yaki nashi ta samu cigaba. Shiyasa Hon. Bomboy Nabardo, yace Masa Babu gudu Babu Jada Baya.

A jawabinsa na Karshe yaja Hankalin sa, Hon. Nasiru Nuhu Rimi da Kar yamanta da Al’umman Yankinsa a Halin wuya Koh Dadi.

Daya Daga Cikin Dattawa na wannan tafiya Malam Abubakar Haji da shauran dattawa sun kara da cewa , Su Basu taba ganin matashi Mai Hazaka irinsa, Sannan sunja Hankalinsa Sosai da yazama Mai Riko da gaskiya da Amana.

Anashi jawabin, Hon Nasiru yafara da godiya wa Allah tabaraka wata’ala da Kuma godiya wa wannan jajirtattun Dattawa na (CMC) din, Sannan sun Nuna Masa Halacci da Karamci dakuma  Nuna Masa goyon Bayan Jama’ah na wannan yanki na Toro Jama’ah.

Sannan yakara dacewa zaizamo Mai Riko da gaskiya da Amana, Sannan Kuma yace Sai ya fidda wannan yanki kunya Insha ALLAH.

Sanan  Daga karshe Yana Baukantan su sanyashi a Cikin Addu’a Don ganin an samu nasarar wanna kujera.

Muna Addu’ar Allah ya tabbatar Masa da Alkairi.

Rahoto
Najibullah Zubair.
08 February, 2022

Leave a comment